Grilled chicken and egg sauce

#SSMK gaskiya girkin nan yayi dadi sosai abin sai wadda yaci iyalina sunji dadin shi kuma sun yaba sosai,uwar gida gwadashi kiji.👌🏻
Grilled chicken and egg sauce
#SSMK gaskiya girkin nan yayi dadi sosai abin sai wadda yaci iyalina sunji dadin shi kuma sun yaba sosai,uwar gida gwadashi kiji.👌🏻
Umarnin dafa abinci
- 1
Yanzu ga ingredients dinmu da zamuyi amfani da su.
- 2
Abu nafarko da zamuyi zamu jajjaga attruhu guda biyu.
- 3
Sannan mu dauko mazubi muzuba oil 3tbspn.
- 4
Se musaka wannan attaruhun da muka jajjaga aciki.
- 5
Sannan musaka gishiri 1/4tspn.
- 6
Se muhadasu mujaya.
- 7
Yanzu zamu dauko namanmu musa wuka mu tsatsa gashi kamar haka.
- 8
Se musakashi acikin wannan attaruhun da muka hada da mai,mujuyashi aciki ko ina yashiga.
- 9
Yanzu gashi mungama hadawa,zamu ajiye agefe mubarshi tsahon awa daya.
- 10
Yanzu zamu dauko pan dinmu musa namanmu aciki,se mukunnan wuta kadan karmusa da yawa saboda namanmu ze iya konewa.
- 11
Zamu dinga kula dashi idan bayan yayi semujuya gaban.
- 12
Gashi yanzu naman mu yagasu,munsaukeshi,se mukasa wuka muka yanyankashi.
- 13
Zamu dauko egg dinmu mukadashi,musa oil 1tbspn acikin pan,semuzuba egg din aciki muke juyawa saboda muna so ya dagargaje.
- 14
Ga yanda muka yiwa egg din.damuka gama se muka ajiyeshi a gefe.
- 15
Yanzu zamu jajjaga attaruhu 3 albasa 2.
- 16
Se mu dauko pan musa oil 2tbspn,semuzuba jajjagenmu aciki,mukunna wuta kadan har se ya soyu.
- 17
Semukawo gishiri 1/3 tspn muzuba aciki mujuya.
- 18
Muzu dauko egg dinmu da muka soyashi muzuba a kai mujuya
- 19
Semuzuba corn
- 20
Sannan carrot
- 21
Sannan greenpeas
- 22
Semu juyasu gaba daya murufe na tsahon minti biyu.idan yayi semu sauke.
- 23
Yanzu mungama, zamu dauko faranti mujera namanmu akai dakuma miyarmu.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

































sharhai