Lemon kankana
Yana da saukin sarrafawa,ga dadi da kara lafiya
Umarnin dafa abinci
- 1
Wa’en nan sune abubuwan da ake buqata wajen yin wannan lemo
- 2
Zaki cire kwallon kankanar ki,ki yanka karas,ki fere bawon cucumber,ki zuba duka a blender se ki yanka lemon tsamin ki ki matse ruwan sa a ciki ki zuba siga da ruwa ki rufe ki markada ya markadu sosai.
- 3
Se ki juye a roba ki sa rariya ki tace iya ruwan kawai ake bukata ki zuba a kofi,zaki iya a haka zaki iya sawa a fridges ya kara sanyi.😋abun ba’a magana
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/10934254










sharhai