Maqlooba rice daga Amzee’s kitchen

Hmmmm ba acewa komai kawai a gwada
Maqlooba rice daga Amzee’s kitchen
Hmmmm ba acewa komai kawai a gwada
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko zaiyi parboiling shinkafa sai ki tsane ki ajiye agefe sai kikawo tukunya ki dora ki zuba mai idan yadanyi zafi sai kisa albasa kidan soyata bayannan sai kikawo ginger nd garlic paste ki zuba ki juya sai kisa attaruhu ki soya zuwa minti biyar
- 2
Sannan sai kisa maggi da black da nasa curry da turmeric najuya sannan nakawo shinkafa na zuba najuya sai da komai ya shiga jikinta
- 3
Bayannan sai na yayyafa ruwan zafi sai na rufeta ta turara shinkenan angama shinkafa
- 4
Shikuma shredded chicken din dafarko zaki yanka kazarki dogaye sannan ki yanka carrot da green paper da onion da red paper duk dogayen yanka
- 5
Sai adora pan a wuta sai asa mai kadan sannan akawo wannan kazar asaka adinga juyawa zatai fari sai akawo ginger da garlic asaka asa maggi a cigaba da juyawa sai asa black paper da star anise asa turmeric a juya
- 6
Sannan sai azuba albasa da carrot
- 7
Sai ajuya idan carrot din yadan risina sai azuba green paper da red paper ajuya a bashi minti 3 angama ba a bukatar ruwa aciki
- 8
Bayan wannan sai sai azo a fere dan kali ayi mai yanka fadi sai a soyashi shima tumatir ayimasa yankan fadi a ajiye
- 9
Sannan sai a samu bowl afara zuba shredded chicken din da dan yawa sannan sai a kawo dankalin a jera bayannan sai a jera tumatir
- 10
Bayannan sai a kawo shinkafar a zuba sai a dansa spoon a daddana sai asamu plate a kifa akan bowl din sai a zare shikenan
Keywords
Similar Recipes
More Recipes























sharhai (2)