Soyayyar doya da sauce
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki samo roba ki fasa kwai,sai ki yanka albasa,kisa maggi,gishiri kadan,mix spices,curry sai kiyi whisking ya game
- 2
Ki aza mai a wuta idan yayi zafi sai ki dauko doya da kika fere ki yanka akwance kika kuma tafasa sai ki sa cikin hadin ruwan kwai sai kisa cikin mai kina soya har ki gama sai ki aje gefe
- 3
Idan zaki hada sauce din zaki jaggaga tattasai,tarugu da albasa, sai ki daka tafarnuwa da danyar citta,sai kisaka mai kadan ga frying pan sai ki yanka wata albasa kisa kisa dakakken citta da tafarnuwa,sai ki zuba hadin tattasai,albasa da tarugu kina juyawa,kisa curry,maggi,gishiri kada ki juya yadan soyu sai ki sauke kici da soyayyar doyarki
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11582128




sharhai