Soyayyen dankalin turawa Mai hadin kwai

Safiyya Yusuf @samgz2703
Yara nason wannan hadi musamman da safe
Soyayyen dankalin turawa Mai hadin kwai
Yara nason wannan hadi musamman da safe
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki fere dankalin ki ki yankashi dogo-dogo ki wanke ki tarare akwando
- 2
Saiki aza Mai idan yayi zafi ki fara suyan dankalinki.Zaki soyashi yayi brawn kadan sannan ki kwashe,haka zakiyi har ki qare suyan dankalinki gaba daya
- 3
Saiki yanka albasa ki fasa kwanki a ciki kisa maggi da gishiri ki kada kwan dakyau sannan ki qara mayarda kwanon suyanki saman wuta sannan ki zuba soyayyen dankalin ki kisa Mai kadan sannan ki zuba kwai ki tabbatar kwan ya zagaye iya inda dankalin yake(kada ki sa wuta sosai gudun konewa)
- 4
In kasa ya soyu saiki juya,idan ya soyu gabadaya saiki juye.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11640156



sharhai