Dankali da kwai
Ummu Jawad @cook_19629753
Yana da sauki wurin yi baya cin lkci sosai gashi baya shan mai masu ulcer ma zasu iya ci ba tare da fargaba.
Dankali da kwai
Yana da sauki wurin yi baya cin lkci sosai gashi baya shan mai masu ulcer ma zasu iya ci ba tare da fargaba.
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki fere Dankali sai ki yanka shi kanana duk yanda kk so sai ki wanke ki daura ruwa a wuta in ya tafaso ki zuba dankalin da gishiri ya Dan dahu kadan sai ki tsane a colander
- 2
Ki jajjaga attaruhu da tafarnuwa ki yanka albasa sai ki fasa kwai ki maggi dasu jajjagen sai ki kada sai ki dauraye frying pan ki daura a wuta ki zuba mai Dan kadan ki zuba dankalin sai ki kawo hadin kwan ki zuba akai kina juyawa a hankali har ya soyu. Aci dadi lfy
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/12172287



sharhai