Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki fara da tankade flour ki juye gishiri sugar da yeast akai, saiki mixing
- 2
Zaki melting butter ya huce saiki juye akai, ki kawo ruwan madaran mai dumi ki juye daiki kara ruwan dumi kadan ki kwaba shi amma yayi laushi kar yayi tauri,
- 3
Daga nan saiki dauko kwabin ki kiyi aiki akansa kiyta kneading kamar minti 20 yayi smooth sosai ko ina saiki sa a bowl ki kawo leda ko kitchen towel ki rufe zuwa awa 1
- 4
Bayan awa1 zakiga yayi doubling ya tashi sosai saiki fito dashi ki qara kneading lyk 10mnts
- 5
Sai kisa wuqa ki raba shi daidai da daidai ki mulmula kowanne into balls, saiki shafe pan din gashin ki da butter ki jera su kamar haka, amma tsakanin kowanne ki bar space, saiki dake rufewa kibashi minti 40 zakiga ya hade duk wannan space din ya kumburo sosai
- 6
Saiki fasa qwai ki tsiyaya egg white shi white din dashi zaki shafe saman bread in ki, saiki saka a oven ki kunna wuta sama da qasa a maaunin zafi 250-300 ki gasa ba tsawon minti 20 shikenan, in kin fito dashi ki shafa ma saman butter narkakke saikiga yana sheqi ki barshi a waje ya huce gabadaya sannan saiki saka a leda ki daure zakiji ya qara laushi.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes






sharhai (5)