Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki wanke naman ragon ki kisa a tukunya. Kisa ruwa dai dai yanda zai dafa miki naman ki
- 2
Sai ki samu tarugun ki da albasa ki wanke kiyi grating sai ki samu dadawan ki ki daka ki zuba a cikin naman ki
- 3
Sai ki daura tukunyan ki a wuta sai ki samu tafarnuwa ki jajjaga sai ki zuba kisamu citta busasha kisa kadan sai kisa maggi da onga ki rufe ki barshi amma kinayi kina duba wa karya kama har yayi laishi romon ki yayi kauri shikenan aci dadi lfy
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/12356427




sharhai