Bread donut

Yana da kyau,kuma ga dadi,ba lalli kullum ta bangare daya zaa dinga cin burodi ba,akwae hanyoyin sarrafashi da dama,abun se wanda yaci😋 #FPPC
Bread donut
Yana da kyau,kuma ga dadi,ba lalli kullum ta bangare daya zaa dinga cin burodi ba,akwae hanyoyin sarrafashi da dama,abun se wanda yaci😋 #FPPC
Umarnin dafa abinci
- 1
Wa’en nan sune abubuwan da ake buqata,zaki samu golden morn dinki ki dakashi ye laushi,se ki samu kwai ki yanka albasa kisa maggi star se ki kada.
- 2
Se ki kawo burodin ki sala daya ki dora donut cutter dinki a akai ki cire shape din
- 3
Se ki sashi a kwan da kika kada idan kika cire se kisa a cikin golden morn din ki shafe duka jikin shi da shi
- 4
Bayan kin gama se ki dora mai a wuta bame yawa ba ki yanka albasa idan ta soyu se ki cire ki saka burodin ki a ciki nan da nan ze soyu indae kin bari mai dinki yayi zafi se ki cire kisa a colender ki tsane.
- 5
Idan ya huce se ki zuba a faranti zaki ki ci a chakuleti,ko kisha da shayi
- 6
Ko kuma kici da ketchup.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes


















sharhai (2)