Dambun kuskus
yanada dadi sosai ki hada shi da kunun aya
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zakisa kuskus a cikin roba wai dan fadi sai ki zuba mai a kai yadan yi yawa maidin sai ki jajjaga attaruku da Albasa ki zuba a kai kisa maggi da gishiri kadan sai ki gyara ganyen zogalai shima ki zuba a kai sai sai ki gyara koren tattase da lawashi ki zuba ki juyasu sosai sai dan ruba ruwa kadan zaki yaryada ruwan ne sai ki dauko madambaci ki zuba ki daura a wuta ki rufe da leda bayan minti kadan ya nuna
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/12715241




sharhai