My signature Masa&sinasir

Sirrin kyakykyawar masa shine kada ki bari qullunki ya tashi da yawa (over raising)
My signature Masa&sinasir
Sirrin kyakykyawar masa shine kada ki bari qullunki ya tashi da yawa (over raising)
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki fara da wanke shinkafar ki saiki cire kopi daya ki tafasa ko kuma ki tafasa ruwa ki juye akan shinkafar ki kofi dayan, ki jiqa sauran xuwa awa 2
- 2
Daga nan zaki hadesu da wadda kika tafasa a markada da kauri
- 3
Ki lura wajen markadawa kar amarkada Akan komai, saiki zo kisa murfi tight ki rufe qullun masarki kibarshi sai ya rage awa daya ko daya da rabi in xaki suya saiki kawo albasa ki yanka aciki ki kawo yeast ki juye kiy mixing sosai sosai
- 4
Shi amfanin yanka albasar a lokacin ita kanta albasar tana saka qullun masa ya tashi dawuri sannan yeast dinki ki tabbstar mai kyau ne
- 5
Bayan awa daya kin daukoshi zakiga yadda ya tashi sai Kisa sugar ki mixing sannan abin suya anan shima ki tabbatar abin suyar masa/sinasir dinki baya Kamawa, Saiki Saka. Mai kowanne gida sannan ki zuba qullun ya dan fi rabin gidan kadan saiki rage wuta ki soya idan saman ya Fara bula-bula saiki juya bayan.
- 6
Shikuma suyan sinasir kina iya qara baking powder saiki samu nonstick frynpan dinki kidan saka mai kamar zaki soya wainar flour in yay xafi saiki xuba qullun da dan dama yayi tudu saiki kawo murfi ki rufe saman frynpan dinki ki bari ya soyu sai kinga gaba-daya saman sinasir din yayi saqa kuma ba sauran farin qullu a sama, ana soya sinasir ne gefe daya Kawai.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes




sharhai (4)