Miyar wake

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Wannan shine karo nafarko da nayi miyar wake kuma naji dadinsa sosai nida iyalaina

Miyar wake

Wannan shine karo nafarko da nayi miyar wake kuma naji dadinsa sosai nida iyalaina

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Wake Kofi daya
  2. Nikakken gyada chokali uku
  3. Alayyafo
  4. Albasa
  5. Manja/mai
  6. Maggi
  7. Curry
  8. Onga
  9. Madish
  10. Tafarnuwada citta
  11. Attarugu
  12. Tumatur guda biyu
  13. Tumaturin leda daya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki gyara wakenki kitsurfa kiwanke kicire bayan tas sannan kizuba a tukunya kisa ruwa kidaura a wuta kisa bakin powder rabin chokali sai kibarta tatafasa sosai har yadahu

  2. 2

    Idan yadahu sai kisauke kijuye a wani kwano sannan kiwanke tukunyar kimaidata kan wutan sai kisa manja kadan da mai idan yayi zafi sai kizuba albasan da kika yanka

  3. 3

    Bayan albasan yasoyu sai kidaka citta da tafarnuwa kizuba kijujjuya sannan kizuba tumaturin ledai kijujjuya kidan soya nadan lkci sannan kizuba jajjagen tumatir da attarugu kijujjuya sai kisa su maggi da sauran sinadaran

  4. 4

    Sannan kidan soyata sai kidauko waken da kika dafab kijuye akai sannan kidan kara ruwa dai dan yanda kikeson yawan miyan sai kijujjuya kibarta yadan tafasa sannan kikawo gyada kiwatsa akai sai ki jujjuya kirage wutan sannan kiwanke alayho kizuba sai kibarta na mintuna kadan sai kisauke

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai

Aysha Humairah Abdullahee
Aysha Humairah Abdullahee @cook_16670127
Ai Hajiya in kin tashi ma ki saka mata shredded chicken ko kisaka biscuit bones wayyo dadi😋😋😋😋

Similar Recipes