Dambun kifi

🤧satin da ya gabata ya kubuce min ban daura girki ba kmr yadda na saba....yau a ankare nk ga aiyuka sun min yawa amma tunanina yana nn.Wannan dambun nayi shi ne wa mahaifina,duk da dan kadan ne kusan kowa ya ta6a anji dadishi sosai.

Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za a gyara kifi a wankeshi ciki da waje,sai a samu tukunya a zubashi da sinadarin dandano da kayan qamshi da albasa ya tafaso(ba sai an saka ruwa ba,ruwan jikinshi zai dafashi)
- 2
A gefe guda an yanka albasa qananu an jajjaga attaruhu,sai a samu kwano a bude kifin a dagargazashi a cire qashinshi
- 3
Sai a hade kifin da kayan miyan a cakudeshi,a zuba sinadarin dandado da garin citta da sauran kayan qamshi a cakude
- 4
A cikin kasko a zuba mai sai a juye hadin kifin ana juyawa a hankali,ayi ta juyawa....zai dau lkc kafin kalarshi ta fara sauyawa
- 5
Ayi ta juyawa,har sai yy yadda mutum yk so....yana da dadi da albasa ko aci a cikin burodi
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

sharhai (3)