Kosan fulawa
Kosan fulawa na musamman ne yana da dadi ga kosarwa.
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko dai zaki tankade fulawar ki sai kisa ka yeast dinki kadan sai kisa attarigun da kika jajjaga tare da albasa, gishiri kadan, Maggi daidai misali sai ki zuba ruwan dumi ki kwaba shi kwabin yayi kamar na fanke.
- 2
Sai ki rufe shi ki barshi a guri mai dumi yayi minti goma sai ki juya shi. Sannan sai ki Dora mai yayi zafi sai ki fara soyawa. ana cin sa da yaji sannan ana cin sa da kuli kuli.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/13658643




sharhai (2)