Kayan aiki

  1. flour
  2. Minxed meat
  3. Arish potato
  4. Carrot
  5. Oil
  6. Spieces
  7. Maggi
  8. Salt
  9. Tomeric
  10. Ginger
  11. Garlic
  12. Butter
  13. Baking powder
  14. Corn flour

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki tankade flour dinki ki saka gishiri maggi baking powder ki jujjuya saiki saka tomeric powder ki kara jujjuyawa saiki saka butter ki mummurza ki zuba ruwa ki kwaba a kalla 10 to 15 minutes saiki rufe.

  2. 2

    Saiki fereye dankali ki wanke ki yanka kanana sannan ki kankare carrot shima ki wanke ki yanka k'anana saiki d'ora fan kan wuta ki zuba mai kad'an in yayi zafi ki zuba albasar da kika yanka kanana kika wanke kiyita jujjuyawa harta fara laushi ki zuba ginger da garlic ki jujjuya saiki zuba mixed meat d'inki ki jujjuya saiki zuba garin citta da masoro ki jujjuya saiki saka carrot da dankalin ki rufe in yayi kamar 10 minutes ki bude ki saka maggi gishiri ki jujjuya.

  3. 3

    Saiki barshi a bude kici gaba da jujjuyawa kamar 5 minutes saiki saka tomeric ki samu corn flour d'inki kamar 1 spoon ki kwaba da ruwa ki jujjuya ki zuba a ciki kidan jujjuya saiki rufe 2 minutes ki sauke saiki d'auko dow d'inki.

  4. 4

    Saiki gutsitstsira Dow d'in ki mulmula da hannu saiki d'an fad'a shi ki saka flour a chaping board ki murza saiki shafa ruwan kwai a bakin flour din ki zuba had'in naman a ciki ki rufe ki mammatse da fork haka zakiyi tayi harki gama.

  5. 5

    Saiki d'aura mai akan wuta in yayi zafi ki saka meatpie d'in inya soyu ki juya d'aya side d'in haka zakiyi tayi harki gama aci dad'i lafiya.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
rannar
Kano
I was born in kano state
Kara karantawa

Similar Recipes