Butter cookies (yanayin narkewa😫♥️)

Wannan shi ma daya daga cikin girkunan maryama's kitchen ne da na dade da adana shi ina son gwadawa,duk da da nazo yin nawa na danyi sauye sauye da ya qara armasar da girkin🤩za a iya cin wnn abu da safe a hada da zazzafan coffee ko kuma duk sanda aka so tare da sassanyan moctail😉kamar yadda nima nayi
Butter cookies (yanayin narkewa😫♥️)
Wannan shi ma daya daga cikin girkunan maryama's kitchen ne da na dade da adana shi ina son gwadawa,duk da da nazo yin nawa na danyi sauye sauye da ya qara armasar da girkin🤩za a iya cin wnn abu da safe a hada da zazzafan coffee ko kuma duk sanda aka so tare da sassanyan moctail😉kamar yadda nima nayi
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za a tatse leda daya ta simas(ko wata butter din,yawanci a 250g suke zuwa),sai a zuba icing sugar ayi amfani da mixer ko whisker a bugashi sosai har sai ya canza kala sannan ya hade jikinshi,sai a zuba majinar bature da qwai da zest a qara bugawa da kyau
- 2
A zuba garin girfa da dan ruwa cokali daya a qara cakudeshi,sai a tankade fulawa da corn flour lokaci daya a cikin kwanon,a hankali in aka tankade rabi aka cakude sai a zuba sauran daga baya a qarasa cakudeshi
- 3
Ba zai yi qarfi sosai ba,sai a samu piping bag ki bude bakinshi ki zura nozzle din ki daidaitashi da kyau sai ki samu kofi mai dan tsaya mara hannu ki bude bakinshi ki zura a cikin kifin,sai ki yi amfani da spatula ki riqa debo hadinki kina maidashi cikin piping bag dinki
- 4
Ki kunna abin gashinki(pre heating) sai ki samu farantin gashinki ki shimfideshi da takarda,sannan ki zo ki zana hadin cookies din a kan takardar kamar yadda yk a hoto,za kuma ki iya yin wani fasalin(da wannan irin hadin nawa,1M nozzle da makamancinshi ba zai miki ba saboda zest din da aka saka zai toshe hanya yasa ya riqa guggutsurewa)
- 5
Ki saka shi a abin gashi(za a iya na gargajiya,nima na fara aka dauke wuta da haka na qarasa)na tsawon minti 10 wutar sama da qasa(150 farenheit)har sai ya fara kalar dan duhu kadan🙌shi knn....
Keywords
Similar Recipes
More Recipes











sharhai