Bhindi masala(miyar kubewa)

Wannan miya shahararriyar miya ce a qasar hindu,mafi buqatuwar kayan amfaninta su ne:kubewa,albasa,tumaturi sai kayan qamshi(spices♨️)an fi cin shi da roti(burodi)samfurin....amma ni na ci tawa da shinkafa ne qasar,yana da dadi sosai...ni da mahaifiyata mun ji dadinshi😋amma yar uwata kamar ta zaneni🤣wai abinci ga dandano har dandano ga qamshi amma na zubawa kayan yauqi😏

Umarnin dafa abinci
- 1
Wadannan su ne kayan da nayi amfani da su,duk na yayyankasu ne a tsaye
- 2
Da farko za a fara da zuba mai cikin tukunya,idan ya yi dumi sai a zuba yankakkiyar ku6ewar,ana soyawa hade da juyawa lokaci daya na tsahon minti biyar,zai fara laushi,sai a hada duka kayan qamshin a zubasu a juya sai a zuba albasa
- 3
A soya na minti biyu,sai a kawo yankakken nama da aka tafasa,attaruhu da bay leaves a zuba,minti daya sai a zuba shambo(za a iya saka guda guda ko a yanka gida biyu) a zuba maggi a juya
- 4
A dan barbada gishiri kadan,a bashi minti daya sai a kawo yankakken tumaturi a zuba a juya...a rage wuta can qasa,bayan minti daya a kashe wutar...miyar tana da dadi sosai wlh.
- 5
- 6
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

sharhai (12)