SOSON KW'AI

Soson qwai kayan dad'i ne gargajiya wadda akasari anfi saninsa daga gidan sarauta, sannan Yana da sauqin sarrafawa da dad'in d'andano a baki.
SOSON KW'AI
Soson qwai kayan dad'i ne gargajiya wadda akasari anfi saninsa daga gidan sarauta, sannan Yana da sauqin sarrafawa da dad'in d'andano a baki.
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki Fara da dasa qwai gaba d'ayan su ad'ana Mazubi Mai fad'i
- 2
Sannan zakiy ta kad'a qwan ki ko kisa mixer sai Kinga ya tsinke sosai, sannan saiki saka sugar da gishiri ki sake mixing sai kinji sun narke
- 3
Anan ana buqatar abin suya Mai girma da Kuma zurfi saikisa Mai dayawa Yayi zafi akan wuta
- 4
Daga Nan saiki kawo rariya ana buqatar Rariya irin Mai manyan qofafin Nan (zaga-zaga) saiki jujjuyata da sauri akan man da yay zafin ta cikin rariyan Zaki na zubo ruwan qwan Kuma kina juya rariyan da sauri shine qwan Yana sauqa cikin Mai zakiga Yayi gida-gida saikiy sauri idan Yayi ja ki kwashe, Haka zakiy da sauran ruwan qwan ki duka sai ya qare👌 aci Dadi lafiya.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes




sharhai (8)