Tuwon shinkafa da miyar wake

#repurstate wannan garkin yanada matukar dadi ga kuma kara lpy na koyeshi ne a gurin aunty
Tuwon shinkafa da miyar wake
#repurstate wannan garkin yanada matukar dadi ga kuma kara lpy na koyeshi ne a gurin aunty
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki jika shinkafa tayi kamar 2 hours sai ki wanke ki zuba ruwa aciki sai ki daura akan wuta ya dahu, idan yayi sai ki tuka sai ki sami leda ki kashe aciki.
- 2
Zaki gyara attaruhu da albasa da tumatir sai ki wanke kisa tafarnuwa da ginger kadan aciki sai ki markada, sai ki yanka wata albasa ki zuba acikin tukunya ki zuba manja da man kuli kadan kadan aciki sai ki daura akan wuta sai ki soya sama sama sai ki kawo kayan miya ki zuba aciki sai ki soya.
- 3
Zaki surfe wake sai ki wanke ki rege ki zuba acikin tukunya sai ki daura akan wuta ya dahu, sai ki juye akan kayan miya sai ki maidashi kan wuta sai kisa maggi da gishiri da curry sai ki juya sai ki bar miyar ta dahu shikkenan kin gama.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai