Shawarma mai nama da latas

Yana da dadi kuma ana iya cinsa akoda yaushe, ko kuma ayima baki shi
Shawarma mai nama da latas
Yana da dadi kuma ana iya cinsa akoda yaushe, ko kuma ayima baki shi
Umarnin dafa abinci
- 1
Na hada kayana dazanyi amfani dasu, nasamu kaskona na wanke, na zuba mangyada, nakawo tafarnuwa, albasa, na soya samasama, na kawo naman dazanyi amfani dashi nasa aciki, nazuba maggi da gishiri, da sauran sinadaran kamshi nasa aciki, naci gaba da motsawa, har naman yayi yadda nakeso, sannan nakwashe.
- 2
Nawanke salad, albasa, da tumatur da ruwan khal, sannan na yan yanka, nahadasu wuri daya.,
- 3
Na dauko greek yoghurt naxuba a wani bowl, nakawo black paper nasa aciki, nakawo lemun tsami shima na matsa aciki na ajiye agefe
- 4
Na dauko shawarma bread dina danayi, nadauko, salad din mai albasa da tumatur nasa aciki, (wasu nasa cocumber ko duk abinda mutum keso)nakawo naman nadora akai, sannan idan za'aci sai azuba hadin danayi na yoghurt sai asa akai sai anade.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai (2)