White rice and stew with plantain & salad

Mrs Mubarak
Mrs Mubarak @maanees_kitchen

Wannan girkin nayishi ne saboda yanada dadinci da rana

White rice and stew with plantain & salad

Wannan girkin nayishi ne saboda yanada dadinci da rana

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Ruwa
  2. Shinkafa
  3. Bandataccen kifi
  4. Tumatir
  5. Tattasai
  6. Tarugu
  7. Albasa
  8. Magi
  9. Gishiri
  10. Farin mai
  11. Plantain
  12. Salad da tumatir
  13. Curry

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da darko dai zaki tanadi kayan bukata, kamar haka

  2. 2
  3. 3

    Zaki fara da daura wankakken tukunyanki a wita kisa ru. Idan ruwan ya fara zafi saiki wanke shinkafarki ki saka aciki

  4. 4

    Zaki bashi dan lokaci yayi tafasa biyu zuwa ukku saiki sauke ki kara wankewa saboda ta rage danko

  5. 5

    Sai ki kara maidawa akan wuta ya ida nuna. Bayan kin wanke zaki barbada gishiri kisa ruwa dai dai yanda zai isa ya ida nunata.

  6. 6

    Sannan ki gyara kayan miyanki kiyi blending dinsu Amman kar ki bari yayi lukui lukui,sannan ki daura akan wuta.

  7. 7

    Bayan kamar minti 5-10 ruwan tumatir dinki ya fara tsotsewa saiki zuba mai acikin blending dinki

  8. 8

    Idan yayi kamar mintina biyar kuma sai zuba baking powder saboda ya kashe miki tsamin tumatir inki sannan manki ya kuma fito,sannan kisa hadin magi dinki

  9. 9

    Zaki gyara bandataccen kifin ki wanke da ruwan dumi saboda kura da kuma kanun kwari.

  10. 10

    Zuwa lokacin miyanki yayi kusa nuna saiki zuba kifin da kika riga kika gyara aciki ki yanka albasa akanshi kafin ki zuba

  11. 11

    Bayan kamar 5minute saiki zuba curry dinki da magi onga ki kashe wuta ki sauke miyan ya hadu

  12. 12

    Mataki na karshe.
    Zaki gyara plantain dinki ki yanka into pieces din shaped dinda kike so sai ki soya a cikin mai.

  13. 13

    Zaki soya har sai yayi golden brown.

  14. 14

    Sai ki wanke salad dinki ki tsane shi a gwagwa 😋😋

  15. 15

    Daga karshe sai ayi batun cin dadi da hannu ko da spoon……
    Finally 😋😋😋😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mrs Mubarak
Mrs Mubarak @maanees_kitchen
rannar

sharhai (4)

Ummu_Zara
Ummu_Zara @ummu_zaraskitchen
@maanees_kitchen gaskiya wannan girkin ya bada kala ƙawata 😍😋👍

Similar Recipes