Donut

Wanan donut din yana da dadi sosai ga laushi sosai sai kun gwada zaku ji dadinsa #teamkatsina
Donut
Wanan donut din yana da dadi sosai ga laushi sosai sai kun gwada zaku ji dadinsa #teamkatsina
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki samu fulawa kisa a roba ki kawo yeast dinki da egg ki zuba kisa flavour
- 2
Bayan nan sai ki murje su ko ina ya hade jikin sa har sai kinga yayi kamsr burus burus haka sai ki kawo ruwan dumi ki dan zuba kadan kina motsawa kina zubawa har sai kinga yana kama maki hannu
- 3
Bayan nan sai ki dauko shi kisa a abun murza fulawa ko tubur dai haka ki kawo butter ki shafa kita murza kina sa fulawa a hannu ki kadan saboda kamu ki murza har na tsawon minti 15 ko sama da hama ki tabbata ya murzu dai sosai yasha bugu
- 4
Bugun da saki masa shi zai saka shi laushi sosai sanan ki dauko ki dinga diba ki mulmula shi yayi round sanan ki kawo tire ki barbada fulawa ko baking paper ki daura shi akai haka zaki masu duka sanan sai ki dauko butter da kika narka ki shafa a saman su
- 5
Sai ki kai guri me dumi ya tashi idan ya tashi sai ki saka mai yayi zafi amma ba zafi sosai ba baa so mai yayi mugun zafi sai ki saka donut dinki ki rage wuta saboda baa son wuta tai masa yawa idan side daya ya soyu sai ki juya dayan ma yayi haka har ki gama
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai (5)