Sinasir me madarar kwakwa

#teamsokoto Sinasir abincin Hausawa ne musamman arewaci, Yana da Fadi sosai ya na da saukin yi Kumar za a iya ci a Karin kumallo, da Rana ko da dare. Sannan za a iya ci da miya, suga, Zuma ko kuli-kuli. Iyalina suna son CIN sinasir 🥰

Umarnin dafa abinci
- 1
Za a jika shinkafa ta kwana a jike, ko kuma ta yi awa 5
- 2
Za a tsame shinkafa a wanke sosai,
- 3
Za a Nika shinkafar tare da dafaffiya da kuma yeast babban cokali 1
- 4
Za a zuba madarar kwakwa a jiya sosai su hade
- 5
Za a rufe a aje a Rana ko wuri me zafi don ya tashi
- 6
Idan ya tashi za a ga ya yi kumfa kamar haka
- 7
Se a zuba baking powder kadan tare da gishiri da suga in ana bukata
- 8
Se a sa kasko a wuta tare da Shafa Mai kadan
- 9
Idan Mai ya yi zafi se a Fara zubawa kadan kamar ludayi data da rabi in karami ne
- 10
A rufe kasko a kuma rage wuta
- 11
Bayan minti biyu a Bude idan Babu kullu a Sama alamun ya yi kenan
- 12
Se a kwashe a mazubi me kyau a rufe,haka za a yi ta yi har kullu ya kare
- 13
Sinasir ya kammala na ci nawa da miyar yaushe kuma ya yi dadi sosai
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

sharhai (3)