Peanut burger
Babyna Tana sonta inayi mata saboda zuwa school
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki gyara gyadarki ki cire bari,ki zuba mata ruwan dumi da Dan gishiri ki tace,saiki shanyata a Rana ta bushe.
- 2
Ki kada kwanki a roba kisa Madara,sugar,Saiki dauko gyadarki ki zubata a babbar roba,ki ajiye flour ki a gefe,Sai kina zuba hadin kwanki akan gyadar kaman cokali uku ki barbada flour itama Sai ki dau robar ki jijjiga su hade,haka zakinayi har Sai hadin kwanki ya kare.
- 3
Daganan Sai ki Dora Mai a wuta kina soyawa baa cika mata wuta.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/15879674




sharhai