Fatan Tsaki
I love fatan tsaki somuch 😋 #MLD
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafari zaki wanke tukunyarki ki daura akan wuta
- 2
Saiki soya manjanki, Daman kin jajjaga kayan miyanki a gefe, saiki zuba cikin manjan ya soyu gaba daya
- 3
Saiki tsaida ruwan sanwanki daidai, ki wanke wake ki zuba ki zuba kayan dandano da nama da tantakwashin nan da kika wanke
- 4
Ki barshi ya dahu sosai sai waken yayi laushi yanda kike bukata,
- 5
Kafin ya dahu Daman kin wanke tsakinki kin yanka alaiyahunki da yakuwa kin gyara gyadarki Sannan kin yanka albasanki
- 6
Sai ki zuba tsakin nan naki tare da gyadarki kinayi kina juyawa sabida kamawa
- 7
Idan ya nuna saiki zuba aliyahu,yakuwa da albasanki yankakke saiki rage wutan kadan yanda zasu turaru
- 8
Shikenan faten tsakinki ya kammala sai ki zuba a kwano a zuba man shanu😋.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16228040





sharhai