Gashin kazar Hausa

Ceemy's Delicious @ceemys_delicious
Wannan girkin na sameshi neh a wajan kanwar mamanmu ranar da naje gidanta ta gasamin naji yayi dadi shineh nace ta koyamin
Gashin kazar Hausa
Wannan girkin na sameshi neh a wajan kanwar mamanmu ranar da naje gidanta ta gasamin naji yayi dadi shineh nace ta koyamin
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko xaki fara daka citta, masoro, kimba da tafarnuwa sannan ki tankade ki ajye a gefe
- 2
Sai ki samu gishiri koh lemon tsami ki wanke kazarki sosaiidan ta wanku sai ki dauko roba mai kyau ki zuba wadannan kayan kamshin da kika daka, sannan ki saka maggi, mai da barkona ki juya.
- 3
Bayan nan sai ki dauko wannan kazar ki safe ta da wannan kayan da kika hada sai ki barta tayi awa 2 koh 3 sannan sai ki gasa shikenan kin gama.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16233905



sharhai (3)