Farin shinkafa da miyar Alayyahu
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko dai zaa daura wuta akan wuta don parboiling shinkafa.
- 2
Bayan ruwan ya tafasa sai a zuba shinkafa yayi kaman minti 5 yana juwaya sai a tsane.
- 3
Sai a sake daura ruwa kadan don karasa nunan shinkafan in ya tausa a juye shinkafan acikin har sai ya nuna.
- 4
Sai a daura tukunya a zuba manja da albasa da Daddawa a dan soya kadan.
- 5
Sai a soya jajjagen kayan miyan tare da gishiri shima na minti kadan in ya soyu
- 6
Sai a zuba alayyahon a ciki tare da tattase guda biyu wanda baa jajjaga ba a rufe zuwa minti 3.
- 7
In yayi sai a zuba yankekken albasa da dandano da kayan kamshi a rufe zuwa minti daya.
- 8
Aci dadi lafiya😊
- 9
Zaa jajjaga tattase da attaruhu da albasa a ajiye shi a gefe.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16320470




sharhai