Umarnin dafa abinci
- 1
Ki samu madambacinki ki saka ruwa a ciki, ki wanke tsakin shinkafarki ki zuba a cikin madambacin,
- 2
Ki saka gyaɗa a sama ki samu fefe ko leda ki rufe bakin madambacin sai ki rufe da murfin tukunyar.
- 3
Bayan shinkafarki tayi rabin dahuwa ki sauke ki saka a babbar roba ki saka zogalenki da albasa attarugu da duk kayan haɗinki
- 4
Da mai sai ki tona har sai sun haɗu sai ki maida tukunya.
- 5
Ki gyara zogalenki da albasa da attarugunki ki jajjaga attarugun gaba daya ki haɗa kayanki.
- 6
Daya dahu zaki ji qamshi na tashi.
A ci lafiya
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16322837




sharhai (7)