Chicken shawarma
Umarnin dafa abinci
- 1
Ki haɗa fulawa, yeast, sugar da salt kisa ruwan dumi ki kwaba sai ki murzashi sosai na minti 5 ki barshi ya tashi
- 2
Bayan ya tashi sai ki raba shi 8 kiyi rolling ki Sa plate da pizza cutter ki yanka edge din dan ya zama circle sai ki gasa a frying pan, bayan ki gama kisa towel ki rufe kar ya bushe.
- 3
Zaki dauko chicken breast dinki(na riga na tafasashi da spices), sai kisa folk ki mutsurstukashi ki cire kashi.
- 4
Ki yanka albasa a frying pan, ki jajjaga tattasai da tarugu, sai ginger and garlic paste
- 5
Ki zuba mai A albasar in ya fara soyuwa kisa ginger sai jajjage kiyita juyawa sai ki zuba naman kazar kisa seasoning dinki kiyita juyawa, kisa ruwan kaɗan kamar 2tbs ki zuba saboda kar ya bushe ki cigaba da juyawa at low heat na minti 5 sai ki sauke
- 6
Ki haɗa ketchup da mayonnaise guri daya, ki yanka cabbage ki wanke ki tsane ruwan ki dauko Irish dinki da shawarma bread da kikayi.
- 7
Ki Fara shafa hadin ketchup kan bread, sai ki zuba naman ki zuba cabbage kisa Irish
- 8
Sai ki nade kamar yadda kika ga nayi, sai kisa wani tsinke ki soka.
- 9
Kisa mu baking pepper kisa shawarman sai ki jera kan frying pan kiyi baking na 5m
- 10
Enjoy 😉
Keywords
Similar Recipes
More Recipes


































sharhai (6)