Stir fry spaghetti
Wnn girkin ga sauqin yi ga kuma dadi.
#tel
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki daura ruwa a pot su tafasa, sai ki karya spaghetti dinki ki saka aciki da green beans. ki barta tadan dahu sama Sama. Sai ki tsaneta a kwando,.
- 2
Kiyi grating tattasai da tarugu,
Ki kankare karas ki yankashi qanana.
Ki yanka albasarki ma - 3
Ki gyara kifinki, ki cire masa kaya.
- 4
Ki daura frypan a wuta, ki saka Mai, ki daka citta da tafarnuwa, ki saka aciki, ki saka thyme, sai ki yanka albasa kadan aciki, su Dan soyu.
- 5
Sai ki saka carrot dinki, ki Dan soyashi sama sama, sai ki saka Albasar da kikayanka, ki saka tattasai da tarugu da kikayi grating
- 6
Ki barsu su soyu, sai ki saka curry da dandano aciki, sai ki juye spaghetti dinki da green beans aciki,ki saka kifinki,sai ki motsa ko'ina y hade jikinsa
- 7
Sai ki rufe, ki Maida wuta a kasa,. Bayan minti 5 sai ki Bude, ki sake motsawa, sai ki rufe.
Ki bata minti 2, sai ki sauke. - 8
Keywords
Similar Recipes
More Recipes






sharhai