Tuwon shinkafa miya danyen kubewa

Inason tuwo Amma baina baina..Amma mr H yanason tuwo sosai zai iya ci yau yaci gobe yaci jibi😄Yayi tafiya Da zai dawo nace mai zan Dafa Masa yace tuwon shinkafa miya danyen kubewa😅
Tuwon shinkafa miya danyen kubewa
Inason tuwo Amma baina baina..Amma mr H yanason tuwo sosai zai iya ci yau yaci gobe yaci jibi😄Yayi tafiya Da zai dawo nace mai zan Dafa Masa yace tuwon shinkafa miya danyen kubewa😅
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko zaki soya manjanki sannan ki zuba ruwa,a cikin ruwanan zaki zuba garin citta dan daidai kar yayi yawa in yayi yawa zaiyi daci,
- 2
Sai kiza garin daddawa,wake,uhuru,dandano sai ki barshi ya nuna sosai da sosai..In ruwa ya kusa tsotsewa zaki kara ruwa yata dahuwa
- 3
Miyanki yana dahuwa kuma sai ki dauko kubewa ki yankashi ki zuba a turmi Ki hada dasu attarugu da albasan kidan jefa gudan kanwa kafan a ciki sai kidaka
- 4
Bayan ki daka sai ki dawo wajen miyanki kisaka biryani masala(optinal ne amma yana dadi gskya)sannan ki kawo kubewan nan kizuba a cikin ruwan miyanki Kisa whisker ko burugali ki kada shi sosai
- 5
Ki rage wuta ki barshi yayi kamar 10mins yana dahuwa kar kk rufe tukunyar amma
- 6
Shikenan miya ya dahu
- 7
Sai ki rage wuta yayi a hankali kinayi kina duba yanayin kaushinsa in ruwa ya kare bai nuna ba sai kara ruwa.
- 8
Zaki wanke shinkafan tuwonku tas sai kisa ruwa akan wuta ki juye shinakfan basai ya tafasa ba haka zakisa da sanyinshi ki barshi yafara tafada in ya dauko nuna
- 9
Inkin tabba yayi laushi sosai da sosai sai kisa muciya ki tuke shi sosai sai ki rufe ki barshi ta turara
- 10
In ya turara sai ki sauke kisake tukuwa sanna ki zuzzub a leda shikenan
Keywords
Similar Recipes
More Recipes










sharhai (2)
muna mishi barka da zuwa.