Soyayyiyar Shinkafa

Zarah Modibbo @Zarahmoddibo_07
Soyayyiyar Shinkafa
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko Zaki zuba mangyada a tukunya ki Saka Bayleaves ki zuba yankakke Albasa ki Dan soya na 2minutes
- 2
Sai ki kawo wankakkiyar Shinkafanki ki Zuba akan Mai din Nan ki soyashi Kamar na 15minutes
- 3
Ki da seasoning kadan Lisa friedrice spice da turmeric sai ki kawo ruwan zafi ki Zuba ki barshi ya dahu bawai yayi laushi ba
- 4
Sannan sai ki kawo wanca shinkafan kizuba ki Kara seasonings to ur taste ki Kara friedrice spice
- 5
Kizuba curry ki Dan sa ruwa kadan ki barshi ya Dan sake dahuwa
- 6
A wani tukunya daban ki Zuba Mai Dan kadan ki Zuba kayan lambunki Dana lissafa Amma Banda Green pepper ki Dan soyasu Sama Sama
- 7
A karshe sai ki kawo yankakke koren tattasai sai ki Zuba ki juya ki barshi ya danyi steaming shikenan kin gama
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16559398





sharhai