Umarnin dafa abinci
- 1
Tankade fulawa a kwano, sikizuba baking powder, da gishiri, da sugar ki gauraya
- 2
Seki dauko butter cokali 2 kisaka ki gauraya
- 3
Seki Kada kwai ki juye aciki
- 4
Seki hadeshi guri daya ki rufe na tsawon minti 10
- 5
Ki dauko tukunya kisaka kifinki aciki, seki saka kayan qamshi, ki tafasa
- 6
Ki cire qayar dake cikin kifin seki faffasashi
- 7
Ki jajjaga kayanmiya, sekidauko tukunya kisaka mangyada a ciki
- 8
Kidauko jajjagen kayan miyan seki zuba a tukunya seki dauko karas dakika grating kizuba
- 9
Seki dauko kifinn ki juye a ciki daganan kizuba sinadaran dandano aciki, idan yahadu seki sauke
- 10
Seki dauko fulawan ki yanka
- 11
Daganan seki dauko rolling pin ki murza, seki debo hadin sauce din ki zuba, daga nan seki nade
- 12
Kisa mangyada a frying pan idan yayi zafi se ki dauko daya bayan daya kisaka a ciki, daganan idan ya soyu ki juya harse ya soyu gaba daya.
- 13
Za a iya cin spring rolls da Lipton ko kuma juice.
Similar Recipes
More Recipes














sharhai