Taliyar indomie da kwai
Amina Ibrahim @meenah_HomeV
Taliyar indomie da kwai
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko zaki dora ruwa a tukunna idan yatafasa seki zuba indomie a ciki
- 2
Seki kawo yankakken karas dinki kisaka
- 3
Seki zuba albasa da jajjagen attaruhu
- 4
Seki zuba jajjagen citta da tafarnuwa ki rufe
- 5
Bayan minti 1 seki bude kisaka sinadaran dandano nacikin indomie ki zuba
- 6
Daganan yana nuna seki juye
- 7
Daga bisani kin dora man gyada a wuta yayi zafi seki dauko fererren dankalin dakika yanka ki zuba gishiri kadan seki soya
- 8
Fasa kwai kizuba maggi kadan da jajjagen attaruhu da albasa aciki ki juya
- 9
Seki dauko frying pan ki zuba mai kadan se ki soya
- 10
Seki juya dayan gefenma ya soyu
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16821153




sharhai