Shinkafa da wake da sauce din manja🥧
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za’a tsince wake se a dora ruwa ya tafasa, za’a iya jiqa waken bayan an tsince shi saboda ya nuna da wuri ko a diga kanwa kadan. se a zuba cikin tafasashahen ruwan se ya dauko dahuwa se a zuba shinkafa dede misali a juya se a barta se ta dauko dahuwa se a tsane ruwan, se a sake maida wani ruwan kadan cikin tukunyar se a maida shinkafa da waken ciki ya karasa dahuwa idan ta nuna ruwa ya tsane se a sauke.
- 2
Se sauce din manja kuma za’a jajjaga kayan miyan ne(attaruhu, tattasai, albasa) se a juye a tukunya a zuba manja a soya se akawo kayan hadi(maggi, gishiri, curry ko thyme) ko wani kayan kamshi wanda ya sauwaqa a zuba a motsa se a sauqe a zuba kan shinkafa da waken.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/7705907








sharhai