Cincin me laushi

Kasancewar ina son cincin yasa nake yinsa akai akai. Yanada dadi Duk dadewar da zaiyi dadi zai kara yi.
Cincin me laushi
Kasancewar ina son cincin yasa nake yinsa akai akai. Yanada dadi Duk dadewar da zaiyi dadi zai kara yi.
Umarnin dafa abinci
- 1
A tankade fulawa a ajiye a gefe.
- 2
A sami roba me tsafta a zuba sukari, kwai da butter, ayi ta juyawa har sai sun hade jikin su.
- 3
A zuba baking powder, flavors, kwakwa da kantu a juya sosai, sannan a kawo fulawar a zuba ana juyawa har sai ya hade ya zama gari.
- 4
A zuba ruwa da kadan kadan ana kwabawa har ya hade jikinsa, kkwabin Kar yayi tauri.
- 5
Sannan a yayyanka fulawar a dunga murzawa ana yankawa.
- 6
A Dora mai a kan wuta a yayyanka albasa Idan yayi zafi sai a dunga zuba cincin din a ciki da kadan kadan ana juyawa har ya soyu sai a kwashe.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes





sharhai