Nadadden nama(beef wrap)

Na koyi wnan girkin gurin chef Fasma daya daga cikin gwanayena nayi amfani da nama sabanin naman kaza da tayi.
Nadadden nama(beef wrap)
Na koyi wnan girkin gurin chef Fasma daya daga cikin gwanayena nayi amfani da nama sabanin naman kaza da tayi.
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki sama naman curry,thyme,tafarnuwa,citta,Maggi,ketchup,mayyonaise da mai kadan ki barshi tsawon rabin awa
- 2
Sai ki kwaba fulawa,yeast,sugar da gishiri,kadan ki barshi ya ninka rabin girmanshi
- 3
Idan yayi ki murza kiyi masa shape mai zagaye ki shafa mai kadan a kasko ki dora fulawan ya gasu kowane gefe.kisa a flask
- 4
Sai ki dora wata tukunyan ki soya naman mai kayan maggi ki ba suya rumus ba ki barshi da ruwa ruwansa.
- 5
Idan ki ka sauke ki kwaba ketchup da mayonnaise guri daya ki shafa a biredin da kika gasa ki zuba naman ta gefe sai ki masa kamar yadda ake nade shawarma.Shikenan sai ci
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai