Wainar gero ta musamman

Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
Kano, Meduguri Road, Tarauni.

Wainar gero tana daya daga cikin abincin hausawa, tanada dadi sosai ta samo asali ne tun a zamanin kakanninmu, wannan shine karo na farko da na gwada yi, sai gashi tayi kyau tayi dadi kowa yana ta santi..#iftarrecipecontest

Wainar gero ta musamman

Wainar gero tana daya daga cikin abincin hausawa, tanada dadi sosai ta samo asali ne tun a zamanin kakanninmu, wannan shine karo na farko da na gwada yi, sai gashi tayi kyau tayi dadi kowa yana ta santi..#iftarrecipecontest

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Awa 3mintuna
8 yawan abinchi
  1. Gero surfaffe gwangwani 6
  2. gwangwaniDafaffen gero Rabin
  3. Yist babban cokali 2
  4. Dakakken karkashi cokali 2
  5. Dakakkiyar kubewa cokali 1
  6. 4Magi guda
  7. Gishiri Dan kadan
  8. 1Albasa Babba guda
  9. Man suya
  10. Kabeji rabi
  11. 2Tumati manya guda
  12. Cucumber
  13. 1Korean tattasai Babba guda
  14. Garin Kuli kuli Wanda ya sha kayan hadi

Umarnin dafa abinci

Awa 3mintuna
  1. 1

    A sami gero a surface a cire dusar sannan a wanke shi a rege a fitar da tsakuwar sai a jika shi na mintuna 30.

  2. 2

    Sannan a yi amfani da blender me karfin markade a markada yayi laushi sosai, ko a kai inji a markado.

  3. 3

    Idan an markado sai a zuba yist a juya sosai a tabbatar ya samu. Sannan a rufe a dakashi a rana ko GU me dumi ya tashi na tsawon awa 2 ko fi.

  4. 4

    Bayan ya tashi sai a dauko za a ga yayi kwai a ciki alamar ya tashi kenan. Sai a kawo karkashi da kubewa a zuba a ciki

  5. 5

    Sannan a zuba dafaffen gero a ciki a juya sosai, sai a zuba albasa da magi da gishiri a juya Idan ya juyi sai a dandano naji Idan akwai tsami sai a saka bakar hoda karamin cokali 1 a juya.

  6. 6

    A Dora tanda (kaskon yin waina) a zuba mai Idan yayi zafi sai a dunga zuba kullin a ci. Idan ya soyu sai a juya gefe. A dunga kwashewa a kwano ko roba ta sha iska har a gama.

  7. 7

    A wanke kabeji, Korean tattasai, tumatir, guriji da albasa a yayyankasu yanda ake so a tsane a kwalanda. Sai a sami kwano a zuba wainar, sannan a barbada mata kuli kuli sannan a yaryada mai.

  8. 8

    Sannan a zuba kabeji, tumatir, Korean tattasai, albasa da guriji. Sannan a sake saka wainar, a barbada kuli a zuba mai sannan kayan kabejin haka za ayi har a zuba yawan da ake so.

  9. 9

    Shikenan sai a rufe. a ci ta da kunu ko da lemo tanada dadi sosai.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
rannar
Kano, Meduguri Road, Tarauni.
cooking is my dream!!!
Kara karantawa

Similar Recipes