Funkaso da miyan kabeji da kaza

Idan dai kika gwada to tabbas ba xaki sake marmarin yin fankaso da wata miyar ba se wannan😍
Funkaso da miyan kabeji da kaza
Idan dai kika gwada to tabbas ba xaki sake marmarin yin fankaso da wata miyar ba se wannan😍
Umarnin dafa abinci
- 1
Funkaso xaki tankade fulawa ki xuba a cikin abinda zaki kwaba ki saka yis gishiri da sukari kadan ki yanka albasar kanana ki xuba ki saka ruwan dumi ki dama da hannun ki se yafee saurim tashi in ya hade ki ajiye minti talatin ya tashi ki dakko ki dora mai a wuta in yai xafee ki soya in kika debo ki dan fadadashi da hannun ki kafin ki xuba ko kiyi amfani da mara ta kwasan tuwo in kika debo seki xuba a kai ki buda shi seki xuba a cikin man ki barshi ya soyu yadda kike so ko yai duhu ko yayi haske
- 2
Miyan kabeji ki gyara kabeji ki yanka kanana ki wanke karas ki goga manya kazar ki ma ki wanke ki yanka kanana ki jajjaga attaruhu da albasar ki yanka tafarnuwa da wata albasar ki bare magin ki ki ajiye seki xo ki hada
- 3
Xaki samu kaskon ki saka mai kadan in yai xafee seki xuba tafarnuwa dinki da kika yanka da kuma abun kamshi wato curry ko thyme idan suka dan soyu seki xuba kazar ki itama su soyu tare in suka ki xuba kayan miyan ki ki saka maggi ki juya se ki dan saka ruwa kadan sudan dahu seki xuba karas da albasar bayan minti 2 kuma seki xuba kabeji ki barshi minti uku 3 shikkenan kin gama
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai