Doya da tomatoes sauce

Wannan girki ne da za a iya hadawa a cikin dan kankanin lokaci.
Doya da tomatoes sauce
Wannan girki ne da za a iya hadawa a cikin dan kankanin lokaci.
Umarnin dafa abinci
- 1
A fere doya, a wanke ta, sai a yanyanka ta a tsaye, a tsane a kwando, sai a barbada gishiri, a daura mai a wuta, a yanka albasa, in ya soyu sai a zuba doyan a cikin, a dan sa ruwa kadan saboda tayi laushi, idan ta soyu zata taso saman man, sai a kwashe.
- 2
A fere bayan plantain, a yanka shi ta tsaye, sai a barbada gishiri, a zuba a Mai me zafi, idan ya soyu za a ga sunyi brown, sai a kwashe.
- 3
Yanda ake tumoto sauce shine, za a wanke kayan miyan, sai a yanka su kana, sai a sa man gyada a wuta a yanka albasa, idan ya soyu sai a zuba yankakkan kayan miyan a Kai, ana juyawa, idan ya fara soyuwa sai a sa gishiri kadan da sinadarin dandano, sai a juya har sai ya soyu Mai ya fito, sai a kashe wutan, a ci da doya, plantain, ko yanda ake so.
Similar Recipes
More Recipes



sharhai