Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki gyara Naman kaza ki tafasa da maggi, gishiri da albasa
- 2
Sannan ki gyara tumatur,tattasai da Tarugu kiyi blending kada kiyishi yayi laushi sosai
- 3
Sai ki aza Mai awuta ki soya namanki,bayan kin qare suyan Naman sai ki rage Mai sannan ki zuba kayan miyanki ki soyasu
- 4
Bayan sun soyu sai ki sa ruwan tafashen nama, zuba soyayyen namanki, ki sa maggi da Curry ki rage wuta sai ki yanka cabbage manya manya ki wanke da gishiri sai ki zuba ki rufe
- 5
Kibarshi kamar 5-7 min sannan ki sauke
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/10696997




sharhai