Pizza me sauki
tana da saukin yi ba wahala kuma ga dadee
Umarnin dafa abinci
- 1
Farko xaki yanka naman kazar ki bada yawa ba kanana ki wanke seki dan tafasa sama sama da gishiri daa masoro in ta dahu seki sauke ki yanka tumatur bada yawa ba albasar ma haka koren tattasai ma haka ba manya ba ba kuma Kanana ba ki wanke ki aje
- 2
Idan cheese dinki gogagge kika siya shikkenan idan kuma ba gogagge vane seki goga shi a abun goga kubewa iya adadin yadda kike so shikkenan seki dakko biredin pizza dinki ki jera kazar ki akai ki jera albasar da tumatur da koran tattasai da kika yanka ki xuba cheese dinki akai ki saka a faranti gashi ki gasa akan 180 na tsawon minti 30 shikkenan se ki yanka kin gama
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/10905296







sharhai