Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko Zaki gyara wakenki ki wanke sannan kinaza dahuwarshi tareda saka kanwa rabin karamin cibi cikin waken don yayi saurin dahuwa
- 2
Saiki gyara tattasai, Tarugu da albasa ki jajjagasu ko ki markada a blender
- 3
Bayan wakenki ya dahu saiki zubashi a kwando don ya tsiyaye,sannan ki mayarda tukunyar ki kan wuta ki zuba Mai bayan yayi zafi saiki zuba nikakken tattasai, Tarugu da albasa ki dan soyasu sama- sama
- 4
Bayan sun soyu saiki zuba ruwa inya tafasa saiki zuba maggi da gishiri sannan ki dauko taliyarki ki zuba kibarta kamar 2-3 mins sannan ki motsa ki zuba dafaffen wakenki a Kai ki sake motsawa sannan ki rufe,bayan kamar 5 mins saiki dauko yankakken alayyahunki ki da kika riga kika wankeshi da gishiri ki zuba saiki rufe
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11032460




sharhai