Dambun kus kus me bushashshen kifi

Maimuna Tike @cook_19004148
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko na juye kus kus a roba na zuba mangyada, jajjagen shambo,sinadaran dandano,zogale,albasa da yawa na gauraya komai ya hade gu daya
- 2
Sai na zuba bushashshen kifina bayan na jika shi da tafashashshen ruwa zafi Sai na zuba aka hadin kus kus din
- 3
Na zuba ruwa kadan a tukunya nasa murfi na rufe na zuba kuskus din akai nasa leda na rufe sannan nasa murfin tukunyan Sai nadora akan wuta na rage wuta
- 4
Ina daga falo nafara jin kamshi alaman yayi kenan
- 5
Na sauke na zuba a plate Zaki iya Kara mangyada da yaji kici
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11033674



sharhai