Wainar shinkafa

Hafsat’s cakes nd more @cook_18602343
Wainar shinkafa
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki wanke shinkafar ki ki jikata ta kwana da safe sai ki zubah da faffiyar shinkafarki ki kai inji amarka kada miki amma kice awanke injin sosai kuma kar ajika ruwa
- 2
Bayan andawo da ita daga markade sai ki zubah yeast ki barshi yah tashi
- 3
Idan yah tashi sai ki yayyanka albasa ki zubah gishiri kadan da sukara yarda kikeso
- 4
Sannan sai ki dauko tandar wainarki sai ki daurata akan abinda kikeyin girki gas ne rishino koh murhu sai ki zubah mai in yayi zafi sai ki dinga zubah kullin wainar idan yah soyu sai ki zuyah bayan idan nanmah yayi saiki kwasheta a kwano
- 5
Zaki iya cinta da miyar taushe
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11050632




sharhai