Shinkafa da wake

Wannan abinci na hausawa ne, ana kiransa da garau garau saboda babu wasu abubuwa mai yawa a cikin hadinsa
Shinkafa da wake
Wannan abinci na hausawa ne, ana kiransa da garau garau saboda babu wasu abubuwa mai yawa a cikin hadinsa
Umarnin dafa abinci
- 1
A gyara wake a wake a tafasashi da kanwa, in ya kusa dahuwa a sauke a wanke bakin ruwan a ajiye waken
- 2
Sai a wanke shinkafa a tafasa, inta tafasa a wanke ruwan shinkafar a ajiyeta
- 3
Sai a zuba ruwa kadan wanda zai isa karasa dahuwar waken da shinkafar a tukunya a zuba gishiri kadan a barshi ya tafasa, sai a zuba waken da shinkafar a jujjuya a rufe
- 4
Bayan kamar minti goma sha biyar sai a duba inyayi laushi kuma ruwan ya tsotse sai a sauke, in kuma ruwan ya tsotse baiyi laushiba sai a dan kara ruwa kadan ya karasa dahuwa
- 5
Sai a zuba mai a kaskon suya a dan zuba yankakkiyar albasa kadan a soya, in albasar tayi ja ko tafara baki sai a sauke
- 6
Sai a zuba shinkafa da wake a plate, a zuba soyayyen mai a zuba yaji da yankakken tumatir da albasa, in anason maggi a barbada aci da zobo mai sanyi
Similar Recipes
More Recipes




sharhai