Umarnin dafa abinci
- 1
A surfa gero, a wanke a rege shi a fitar da tsakuwa, sannan a jika shi ya kwana. Bayan ya jika sai a markada shi yayi laushi.
- 2
A hada filawa tare da yeast a zuba a cikin markaden a barshi ya tashi tsahon awa daya da rabi.
- 3
Bayan kwabin ya tashi za'a zuba sugar da baking powder da karkashi da gishiri a juya.
- 4
A zuba mai a kaskon suya yayi zafi sai a sa cokali ana diban kullin ana zubawa a mai a soya. Aci da kuli -kuli. Idan ana so za'a iya soyawa a tandar waina.
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11612407












sharhai