Potatoes ball

Wannan girki yanada dadi musamman don karyawa da safe #Kadunastate
Umarnin dafa abinci
- 1
Ki fere dankalin turawa, ki tafasa da gishiri, saiki dagargazashi yayi laushi amman karya zama kamar sakwara
- 2
Ki zubawa nikakken nama kayan kamshi da Maggi da albasa ki dan cakudashi
- 3
Ki zuba mai kadan a abin suya saiki zuba tafarnuwa ki dan soya kadan ki zuba jajjagaggen attaruhu, Sai hadin nama ki barshi ya dahu koya soyu saiki sauke
- 4
Ki zuba fulawa a cikin dankalin da kika dagargaza da kurkur ki juya sosai
- 5
Saiki rika mulmlawa kina yin huda a tsakiya kina zuba hadin nama kina mulmlawa harki gama
- 6
Saiki zuba fulawa a faranti, garin busashshen burodi daban, fasa Kwai daban
- 7
Ki dora mangyada a wuta, kina saka ball din nan a fulawa Sai ki tsoma a Kwai Sai a saka garin busashshen burodi Sai a soya a mai in yayi zafi. Anayi ana dauraye hannu a ruwa yanda za a mulmula da sauki
Similar Recipes
More Recipes



sharhai