Chicken Shawarma
Umarnin dafa abinci
- 1
A fereye dankali,a wanke a datsa shi a barbada gishiri kadan,a saka mai a wuta idan yayi zafi a zuba dankali a ciki a soya.
- 2
A wanke kirjin kaza a yankashi kanana,a dora a wuta a zuba onga,attaruhu,albasa,tafarnuwa,mai,kori da kayan kamshi,ayi ta juyawa har ya dahu sai a sauke.A hada ketchup cokali 3 da mayyonnaise cokali 3 a juya sosai.
- 3
Wadannan sune kayan da na hada nayin wannan chicken shawarma
- 4
A dauki bread daya,a shafa masa hadi ketchup da mayyonaise,a zuba kabeji da kokomba
- 5
A saka karas,soyayyen dankali da nama,sai a nade ta,a jera a cikin abun dumama abinci,idan yayi zafi sai aci
- 6
Aci dadi lfy😋🤤😘😍
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/12504532


















sharhai