Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki samu garin alkaman ki me kyau Wanda aka niqa kika tankade sai ki sa a kwano babba sai ki kawo flour ki ki zuba ki kawo yeast da gishirinki kadan ki zuba sai ki zuba mai
- 2
Sai ki samu ruwa ki kwaba shi karyayi ruwa sosai kuwa kar yayi kauri
- 3
Sai ki buga tsawon minti 10 zuwa 15 sai ki rufe ki barshi ya tashi
- 4
In ya tashi sai ki samu gwangwani ki shafa mai a jiki sai ki kawo kwabin nan naki ki zuba
- 5
Sai ki samu ruwa kisa a tukunya ba dayawa ba yanda gwangwanin zai zauna sai ki jera sai ki samu Leda ki rufe sai ki kawo murfin tukunya ki rufe sai kisa kan wuta amfanin rufewa yanda tiririn baze fita ba ki barshi har sai ya dahu
- 6
Shikenan ana ci da miyan taushe
- 7
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/12928191








sharhai